By Abbas Yakubu Yaura
Dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, da kuma malami daya na makarantar, sun samu ‘yanci bayan shafe watanni shida da yin garkuwa dasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar 17 ga watan Yuni, shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga daga dajin Rijau da ke makwabtaka da jihar Neja, sun kutsa cikin makarantar tare da yin garkuwa da dalibai da ma’aikata.
‘Yan bindigar wadanda rahotanni suka ce sun mamaye makarantar ne a kan babura, sun yi galaba a kan jami’an tsaron da ke kasa, inda suka kashe dan sanda a cikin lamarin.
Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya yi watsi da tattaunawa da kungiyar da ke neman kudin fansa.
Watanni hudu bayan sace su, an sako malamai uku da dalibai 30 amma babu tabbas ko an biya kudin fansa.
A ranar Asabar din da ta gabata ne mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya tabbatar da sakin wasu dalibai 30.
“A yau Asabar 8 ga watan Janairu, 2022 dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri da malami daya sun isa Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan an sako su. Za a yi musu gwajin lafiya tare da tallafa musu yayin da zasu sake haduwa da iyalansu.”
Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba shekarar 2021, an sako dalibai 30 na wannan makaranta tare da kawo su Birnin Kebbi don sake haduwa da iyalansu. ban da wasu da aka sake su a baya ga iyayensu.
“Muna godiya ga dukkan hukumomin tsaro da wadanda suka taimaka wajen ganin an sako ‘yan matan, yayin da muke taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar da aka samu.”
Yawan hare-haren da ake kaiwa ya zama abin damuwa ga ‘yan Najeriya ganin yadda kungiyoyin da ke dauke da makamai ke kai hare-hare a fadin kasar duk kuwa da tabbacin da gwamnati da jami’an tsaro suka yi.
A daya daga cikin irin wadannan hare-hare, wanda ya faru a jihar Zamfara, an kashe mutane sama da 143 ta hanyar wasu ‘yan gudun hijira.
Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya sha alwashin cewa za a binciki wadanda suka kashe su.