Daliban Kwalejin fasaha ta Rufus Giwa dake Owo a jihar Ondo sun gudanar da wata zanga zanga, bayan da wani dalibi dan aji daya rasa ransa, sakamakon harbin bindiga da ya samu a jikinsa.
Dalibin mai suna Folarera Ademola ya samu harbin ne bayan da jami’an tsaron Amotekun suka harbe shi tare da ji masa raunuka, lamarin da ya kara fusata daliban har ta kai ga sun fita zanga zangar.
Kazalika daliban sun baiwa gwamnatin jihar awanni ashirin da hudu, don ganin ta dauki matakin daya kamata ga jami’an, da kuma batun diyya ga yanuwan dalibin.
Da yake ganawa da manema labarai a madadin daliban shugaban daliban kwalejin Olorunda Oluwafemi, ya ce jami’an tsaron Amotekun ne suka harbe yaron yayin da yake tsaye a kofar gidan su, ranar 27 ga watan Yuni.
Da yake Karin haske kan wannan batu kwamandan rundunar Amotekun a jihar Ondo Mr. Adetunji Adeleye, yace sun samu wannan labarin ban takaaicin, kuma suna ci gaba da kokarin ganin sun dauki matakin da ya kamata.
A karshe ya bukaci daliban kan su kwantar da hankulan su, don kuwa ba za su bar duk wanda ke da hannu cikin wannan lamari ya tafi haka ba.