Yan bindiga sun saki Dalibai 15 na makarantar Bethel Baptist dake jihar Kaduna.
Idan za’a iya tuna wa, Dalibai 28 yan bindigan suka saki a ranar 25 ga watan Yulin Shekarar 2021, bayan biyan kudin fansan da ya kai naira milliyan hamsin.
Tun da fari dai yan bindigan sun yi garkuwa da Dalibai 121 ne a Makarantar, kamar yadda Shugaban kungiyar Baptist na jihar Kaduna Rabaran Ishaya Jangado ya bayyana, a ranar 5 ga watan Yulin Shekarar nan, wanda kuma shi ne Shugaban makarantar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta kama wanda ya sace Dan makwabcin shi
Yan bindigan sun afka makarantar ce, da ke Unguwar Damishi dake Babban hanyar Kaduna zuwa Kachia na karamar hukumar Chikun, da musalin karfe 2 na daran ranar.
Kazalika Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab ya tabbatar da sakin daliban guda goma sha biyar, a daran jiya Asabar.