Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, Aminu Lawal, wanda aka fi sani da Aminu Kano, da kuma Murtala Dawu, wanda aka fi sani da Mugala, wadanda aka ce mambobin kungiyar masu Garkuwa da mutanene mai suna ‘Yellow Ashana’, sun yi magana a kan yadda suka taimaka wajan yin wani mugunyar garkuwa da wasu dalibai 140 na makarantar Baptist High. Makaranta dake Jihar Kaduna, da dalibai 16 na Jami’ar Greenfield da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja a shekarar 2021 a lokacin baje Kolin su da ‘yan sanda suka yi, inda wakilin Jaridar Punch ABIODUN SANUSI ya halarci wurin.
Mutane nawa ne ’yan kungiyar ku suka sace a lokacin gudanar da ayyukan?
Lawal: Mun yi garkuwa da jimillar Dalibai 140 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist. Makarantar Sakandare na nan dake unguwar Kujama, a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia. Haka kuma mun yi awon gaba da dalibai 16 a wata makaranta da aka fi sani da Jami’ar Greenfield, wadda ke kan titin Kaduna zuwa Abuja, kusa da masana’antar abinci kaji ta Olam, wadda ba ta da nisa da garin Kaduna.
Yaushe kuka sace daliban?
Lawal: Mun sace dalibai 16 na Jami’ar Greenfield a watan Mayun shekarar 2021, yayin da muka sace daliban Bethel Baptist High School a watan Yuli na wannan shekarar barar.
Dalibai nawa ne kungiyarku ta kashe?
Lawal: Mun kashe biyar daga cikinsu suna cikin kogonmu. Mun kai wasu dalibai mata daji, muka yi musu fyade, sannan muka bindige biyar daga cikinsu har lahira kafin mu karbi kudin fansa daga iyalansu.
Me ya sa kuka yi wa dalibai fyade da kashe su?
Dawu: Mun kashe biyar daga cikin wadanda aka yiwa fyaden ne, bayan mun yi wa ‘yan matan fyade a daji saboda an jinkirta biyan kudin fansa. Don haka, mun yi haka ne don mu tsoratar da daliban da kuma sanya tsoro a cikin su.
Ta yaya gungun ku suka sami damar gudanar da aikin cikin nasara?
Dawu: Aikin hadin gwiwa ne. A lokacin ayyukan Greenfield da Bethel Baptist High School, mu daga ƙungiyar gungun Yellow Ashana muna aiki tare da masu garkuwa da mutane daga wasu sansanonin na daban daban.
Wani aiki ne kungiyar ku ta yi?
Dawu: A shekarar 2021, ’yan kungiyarmu karkashin jagorancin shugabanmu, Yellow Ashana, mun yi garkuwa da wasu ‘yan sanda biyu tare da kashe wani dan banga daya.