Dalilan da suka sanya na Janye daga Takarar Gwamna — Malami
Duk da rahoton cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da murabus na Ministocin sa, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya jaddada cewa bai ajiye mulki.
A maimakon haka, Malami yace ya janye daga yin Takarar Gwamnan Jahar Kebbi a Shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojojin Kasa Da Kasa Sun Kashe ‘Yan Ta’addar Boko Haram,ISWAP 300 A Tafkin Chadi
Antoni-Janar ya bayyana haka daga Bakin Mai Taimaka masa akan Kafafen Yaɗa Labaru Dr. Umar Gwandu.
“Malami nada damar da zai zaɓi abinda yaga dama akan ra’ayin shi na tsayawa takarar Gwamna.
“Abune daya danganci ra’ayin rayuwa, kuma damar ɗan adam tunda bai karya doka ba.
Comments 1