Ɓangaren shugabancin Jam’iyyar APC na Jahar Zamfara wato Sanata Kabir Marafa yace zai cigaba da kasancewa a Jam’iyyar duk da irin yadda aka so fusata shi domin barin ta.
Marafa ya bayyana haka a lokacin tattaunawa ta wayar tarho da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Damfara Ta Yanar Gizo Sun Kashe Wasu Masoya 2 Da Abokinsu Guda A Jihar Ondo
Yana maida martani ne akan wata jita-jita cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki na ƙoƙarin ya ɗauke shi da tsohon Gwamnan Jahar Zamfara Abdul’aziz Yari zuwa Jam’iyyar PDP.
Sanatan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattijai ta takwas, yace yayi taro dashi da Yari, amma wannan taron ko kaɗan babu wata tattaunawa da suka yi na batun komawarsu PDP.
Marafa yace “tsohon shugaban Majalisar Dattijai zaije Kaduna domin halartar ɗaurin Aure, sai ya kirani in bishi tunda yasan ina zaune a Kaduna.
“Sai muka tafi Kaduna a tare, sabudda a lokacin ina Abuja a sa’ilinda ya kirani.
“Tsohon shugaban Majalisar Dattijai ogana ne. Yana son in raka shi zuwa ɗaurin Aure da wani Malami ya shirya.
“Malamin ya bada ɗiyar shi aure a ranar Juma’a, sai ya kira Saraki, da Yari, amma Ni bai gayyace ni ba.”
Ya ƙara dacewa, “bana son ace wani ne ya janye ni zuwa PDP, domin idan ina so, Ni da kaina zanyi ba tare da wani yayi ƙoƙarin kaini ba.
“Nayi aiki tuƙuru wajen gina APC a matsayina na mai ruwa da tsaki. Lokacin ina a kujerar Sanata.