Tsohon Gwamnan Jahar Sokoto Attahiru Bafarawa yace Gwamnan Jahar na yanzu Aminu Tambuwal yafi cancanta ya zama Ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaɓe mai zuwa.
Bafarawa ya bayyana cewar irin sirrin siyasar Tambuwal daya ke da shi a baya, da kuma kwarin gwuiwar sa na haɗa mutane, ya sanya yafi kowa cancanta ya zama Ɗan takara a PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Edo Obaseki Ya Dora Laifin Rashin Tsarin Kiwon Lafiya Kan Rashin Shugabanci Na Gari
Ya bayyana haka a neman shawarwari da Tambuwal ya yi dake da manufar tsayawa takara a Jam’iyyar PDP a garin Birnin Kebbi, Jahar Kebbi.
Bafarawa yace kasancewar sa Lauya kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ya sanya Tambuwal yafi cancanta ya zama Ɗan takarar shugaban Ƙasa na PDP.
Ya bayyana cewar Tambuwal zai iya kasancewa a kowane ɓangare na iko idan aka bashi dama a Najeriya.
“Tambuwal bawai Ɗan Majalisa ba, lauya ne, wanda zai iya aiki a ɓangaren Shari’a, kuma yanzu shine Gwamna a wa’adin sa na biyu.