Ƙwararrun Likitocin Zuciya na yara sun yi gargaɗin cewa, ƙarin yara, musamman waɗanda suka fito daga gidan masu hannu da shuni, suna samun hawan jini.
Acewar su, rayuwa marar tsafta da suke sanya yaran su, zai iya zama shine babbar matsalar da zata haifar da hakan.
Masanan sun yi nuni dacewa, sha’awar ciyar da yaran da sauri, tare da haɗa shi da hatsi, ba tare da barin su suna yin wasa ba, to wannan ne dalilin da zai sanya abincin sai ya sanya yaran ƙiba da wuri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Oyo Zata Fara Kamo Masu Yi Wa Mata Kaciya – Kwamishina
Ƙwararrun Likitocin Zuciyar Yaran sun bayyana cewa, matsalar hawan jini ga yara ba abu bane mai sauƙi da za’a iya magance wa kamar na manya, sai suka buƙaci yara dasu zama masu kula domin gane alamun ga yaran su masu matsalar.
Sun shawarci a riƙa duba hawan jini ga yara tun suna da shekaru 3, yana mai cewa dole yara zasu maida hankali ga duk wani canji ga yawan sugar Yaran su.
A cewar Mayo Clinic, hawan jini a yara shine zai kasance sukari na jikin su yakai kashi 95 ko sama da haka.
Mayo Clinic ya bayyana cewar duk da cewa babu wata alama ta hawan jini ga yara, iyaye dole su zama masu kula akan ciwon kai, amai, da zawo, da ciwon ƙirji, da da ƙarancin numfashi ga yara, yana mai cewa zasu iya zama suna da hawan jini.
Dayake magana da jaridar Punch, Farfesa a kwalejin nazarin lafiyar mutane na Jami’ar Benin Wilson Sadoh yace iyaye suna da buƙatar su riƙa kula da hawan jini da yara suke samu.
Sadoh ya alaƙanta hawan jinin yara a matsayin cin abinci ba tare da gudanar motsa jiki ba.
Yace suna cin abinci da yawa na soda da meat pie da sauran su, wanda hakan ne ke sanyawa suyi ƙiba.