Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta kama wani shahararren dan kasuwa , Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana, bisa zargin karkatar da kudade da kuma kaucewa biyan haraji.
Wata majiya da ke kusa da Hukumar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa mai kulob din haifaffen Anambra, wanda ya isa hedikwatar Hukumar EFCC da ke Jabi, Abuja, da tsakar ranar Litinin, yana nan a Hukumar.
Zarge-zargen da ake yi wa Obi Cubana ba su bayyana ba, sai dai wata majiya ta bayyana cewa ana zarginsa ne da almundahanar kudade da kuma zamba a haraji.
Majiyar ta ce, “An kama Obi Cubana ne aka kai shi hedikwatar EFCC a ranar Litinin da yamma bisa zargin karkatar da kudade da kuma zamba a haraji.
Majiyar ta ce “Jami’an tsaro suna gasa shi yayin da muke magana.”
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, lokacin da NAN ta tuntube shi, ya ki cewa komai, yana mai cewa “har yanzu ba a yi masa bayani ba game da batun ba.”