Kotun sauraren daukaka kara mai mazauni a birnin tarayya Abuja ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri.
Hakan ya biyo bayan karar da jam’iyyar ANDP ta shigar gaban kotun inda ta bukaci da ta soke zaben saboda cire ta da aka yi cikin jerin jam’iyyun da za su yi takarar zaben na 16 ga watan Nuwamban 2019.
A lokacin da yake yanke hukunci, Alkali Yunusa Musa ya karbi korafin jam’iyyar ta ANDP inda ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya da ta sabunta gudanar da zabe nan da watanni uku masu zuwa.
Gwamna Diri na Jam’iyyar PDP shi ne wanda ya lashe zaben bayan kotun koli ta sauke gwamna David Lyon a matsayin zababben gwamna awa ashirin da hudu kafin a rantsar da shi.
Kotun kolin ta yanke hukuncin ne bisa dogaro da cewa mataimaki