Fitaccen Malamin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bada labarin abin da ya gamu da shi a yayin ziyarar da ya kai sansanonin ‘yan bindigar da ke jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Gumi wanda ya damu da karuwar matsalar tsaro a yankin arewa maso yammaci, ya ziyarci tungar maharan tare da rokon su da su rungumi zaman lafiya.
A lokacin da yake yi wa gwamnan Zamfara Bello Mutawalle bayani a gidan gwamnati da ke birnin Gusau a ranar Alhamis, shahararren malamin ya ce, ‘yan bindigar sun zama ‘yan ta’adda ne sakamakon yadda jama’ar jihar ke daukar su.
Malamin ya roki gwamnatoci a dukkanin matakai da zu cimma zaman lafiya da ‘yan bindigar, yana mai cewa, tattaunawa ita ce zabi da ya tilo don kawo karshen matsalar.
“A mafi akasarin sansanonin ‘yan bindigar da Fulani da na ziyarta a Zamfara, na fahimci cewa, ba komai ke faruwa ba a jihar illa ta’addanci.” In ji Gumi.
Malamin ya kara da cewa, “Wasu mutane na da ra’ayin yakar tare da kashe ‘yan bindigar, amma abin da muka fahimta shi ne cewa, akasarin su jahilai ne da ke bukatar ilmantarwa da wayar da kai.”
Sheikh Gumi ya ce, “mafi yawan ‘yan bindigar da ya hadu da su sun zama miyagu ne saboda hare-hare da razanar da suke fuskanta daga kungiyar mayakan sa-kai”, inji shi.