Dalilan daya sanya Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya
Babbar Kotun Jihar Kano karkashin Mai Shari’a Usman Na’abba ta yanke wa mai Mallakin Makarantar Noble Kids College, Abdulmalik Muhammmad Tanko, da wani Hashimu Isyaku 38, 38, mai shekaru 38, hukuncin kisa ta hanyar rataya, a dalilin sacewa da kashe Hanifa Abubakar Ɗaliba mai shekaru biyar.
An yanke waɗanda suka taya shi aikata laifin hukuncin shekaru 5 kowannensu bisa laifin haɗa baki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun hallaka Ƴan ta’adda 30 da suka kai wa sojoji hari — DHQ
Sun haɗa baki tare da yin garkuwa da marigayiyar daga Gidauniyar Sheikh dahiru bauchi da aka kashe tare da binne ta a wani kabari mara zurfi a makarantar share fage ta arewa maso yamma da ke Kwanar Yan Ghana a karamar hukumar Nassarawa a Kano.
Abdullahi Lawan ya gabatar da shaidu 8, kuma ya gabatar da hujjoji 14.
Shaidu sun hada da: mahaifiyar marigayiyar, Murja Suleiman Zubair, jami’an DSS da suka kama Abdulmalik, da kuma jami’an ‘yan sanda sun binciki lamarin.
Hujjojin da aka gabatar ya hada da: bayanan ikirari na wadanda aka yankewa hukuncin, hoton mamacin, hijabi, lambar makarantar Islamiyya da dai sauransu.
Sai dai kuma mai gabatar da kara ya gaza tabbatar da tuhumar da ake wa Fatima da aikatawa, amma an yanke masa hukuncin daurin shekara 1 bisa laifin hada baki da kuma shekara 1 kan yunkurin aikata laifi