Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa; daga cikin dalilan da ya sanya Nijeriya ta rufe kan iyakarta na wucin gadi da kasar Jamhuriyyar Benin saboda ayyukan bata gari ta shigo da shinkafa ta barauniyyar hanya duk da haramtawa da kasar ta yi.
Rahotanni sun nuna cewa; an iyakar Seme ne tun bayan umurnin da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe iyakar na wucin gadi, inda aka kai dimbin jami’an tsaro domin bai wa iyakar tsaro na musamman.
Shirin wanda aka yi take da ‘Ex-Swift Response’, ya hada jami’an Kwastam, hukumar lura da shige da fice, jami’an tsaron ‘yan sanda da na soji da hukumomin tsaro na farin kaya wanda ofishin bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro shawara.
Shugaban kasar ya bayyana wadannan dalilai ne a taron da yake ci gaba domin bunkasa nahiyar Afrika a birnin Yokohama na kasar Japan a ranar Laraba. Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa; shugaban kasar na ci gaba da nuna damuwa na yadda ake shigo da shinkafa ta barauniyyar hanya cikin Nijeriya.
Shugaban kasar ya ce shigo da shinkafar babban barazana ne da shirin ciyar da kasarnan ta hanyar dogaro da kai da gwamnati ta fito da shi a bangaren noma. Ya ce; a yanzu da mutanen kauye suka fara komawa gonaki domin komawa gona, ya ce; Nijeriya ta tara dimbin kudi wanda ba don haka ba da Nijeriya ta kashe kudin wajen shigo da shinkafa. Ya ce; ba za su ci gaba da zura ido ana safarar shigo da shinkafa cikin kasarnan ba a irin wannan yanayin.
Shugaban kasar ya tabbatar da cewa; an rufe iyakar kasar ne na wucin gadi, domin bai wa jami’an tsaron kasarnan damar bullo da hanyoyin magance masu safarar shigo da kayayyakin da aka haramta shigo da su. Da yake amsa tambaya akan wahalar da za a fada dangane da rufe iyakokin kasar, shugaban kasar ya ce zai duba yiwuwar bude iyakar na dan wani lokaci a nan gaba.
Ya kara da cewa; za su tattauna da kasashe Benin da Nijer domin bullo da hanyar dakile ci gaba da safarar shinkafar a iyakokin kasashen.