Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya bayyana cewa jami’an gwamnatin tarayya sun tuntube shi da wasu gwamnonin kan hanyoyin da za su sasanta ba tare da kotu ba kan sabuwar manufar kudin Naira.
Sai dai ya yi watsi da tayin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.
Ya ce gwamnatin tarayya ta ba da shawarar a ba da izinin amfanin tsoffin takardun kudi na Naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu. A maimakon haka, gwamnonin su janye kararrakin da jihohinsu suka shigar a gaban kotu.
KARANTA KUMA Wasu Kusoshi A Fadar Shugaban Kasa Na Yiwa Tinubu Zagon Kasa – El-rufa’i
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Nasir El-Rufai, a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Laraba, ya ce rahoton na cewa kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da gwamnatin tarayya sun gudanar da taro a safiyar yau Laraba gabanin zaman kotun kolin kasar a ranar Laraba karya ne.
Gwamnan ya ce ba a samu irin wannan ganawar ba sai dai an yi ta tattaunawa ta wayar tarho inda jami’an suka bayar da rangwame na barin tsohon takardar kudi na Naira 200 ta ci gaba da yawo yayin da gwamnonin suka janye karar.
A cewar ElRufai, gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa a halin yanzu babban bankin Kasa na lalata tsofaffin takardun kudi na manyan kudade na Naira 500 da Naira 1,000.
“Sharuɗɗan da suka gabatar shi ne don ba da damar tsohuwar takardar Naira 200 kawai ta ci gaba da kasancewa a kan doka kuma CBN zai rarraba shi har zuwa 10 ga watan Afrilun 2023,” in ji shi.
Ya ce an ki amincewa da wannan kudiri domin rike tsofaffin takardun ba zai magance kalubalen tattalin arziki da karancin kudin Naira da ya haifar ba.
Idan za a iya tunawa, Jihar Kaduna ta Mista El-Rufai, tare da jihar Kogi da kuma jihar Zamfara sun shigar da kara a gaban kotun koli kan tsarin kudin kasar.
Jihohin da suka hada da wasu bakwai daga baya, sun bukaci kotun koli da ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kudi. Sai dai duk da hukuncin da kotun ta bayar na wucin gadi, babban bankin ya dage kan wa’adin, don haka ya ci gaba da fuskantar karancin kudade saboda sabbin takardun ba su isa ba.
Bayan zaman kotun kolin a ranar Laraba, kotun ta dage zaman har zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci kan manufar.
Zanga-zanga dai na ci gaba da girgiza garuruwa da dama a fadin kasar inda bankunan kasuwanci ke fuskantar hare-hare.
A Wani Labarin Kuma Ku Zabi ‘Yan takarar Da Kuke So Ba Tare Da Tsoron Kowa Ba – Buhari ga ‘yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar da suke so a zabe mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya ce ‘yan kasar nan su yi zabe ba tare da tsoro ba.