Babbar mai tallafa wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kafafen sada zumunta na zamani Lauretta Onochie ta bayyana cikakken dalilin da ya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza halartar Jana’izar Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan Hafsoshin tsaron Najeriya da suka rigamu gidan gaskiya a ranar Juma’ar da ta gabata.
Jama’a da dama musamman a Kafafen sada zumunta na zamani sun yi ta sukar lamirin shugaban kasar na ƙin halartar taron jana’izar mamatan wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.
Sai dai cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na Facebook a ranar Lahadi Onochie ta ce ga shugaban kasa ya halarci wani taro wanda zai gudan a wajen fadar shugaban kasa dole sai abun ya kai awa 48, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanarda.
Ko da yake Mai tallafawa Shugaba Buharin ta ce ita ma kanta ba ta san da wannan doka ba sai da wani mai suna Muhammad Yusuf ya wallafa, to amma lallai wannan shine ke zama dalilin shugaba Buhari na ƙin zuwa jana’izar.