Mai horar da Real Madrid Carlo Ancelotti na fuskantar kora idan har ya kasa samar da sakamako mai kyau cikin sauri.
Abubuwa sun taɓarɓarewa Real Madrid tun bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya, inda yanzu Barcelona ta basu tazarar maki 8 a gasar lashe kofin La Liga na wannan kakar.
KU KARANTA KUMA: Matar Aure ta raka mijinta wajen neman na maggi, ta zage damtse anyi da ita
A cewar rahoton jaridar Sportsbrief, kujerar Ancelotti na tangal-tangal idan har ya kasa lashe kofin FIFA Club World Cup, a wannan ƙarshen makon mai zuwa, wanda za a buga a ƙasar Morocco.
Mahukuntan Real Madrid sun fara cire rai kan cewa kocin zai yi abin arziƙi, duk kuwa da a kakar bara ya lashe kofukan La Liga da na nahiyar zakarun turai wato UEFA Champions League.
Real Madrid za su fafata da kulob ɗin Al Ahly na ƙasar Egypt a wasan dab da na ƙarshe a gasar Club World Cup, wanda za a yi a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu.
A halin da ake ciki, lashe gasar za ta yiwa Carlo Ancelotti wuyar lashewa saboda jinyar da manyan ƴan wasan sa ke fama da ita.
Ƴan wasan irin su Karim Benzema, David Alaba, Ferland Mendy, da Daniel Carvajal ba zasu taka leda ba a wasan da kulob ɗin zai yi Al Ahly.
Ɗanwasan Ƙwallon Ƙafa Na Najeriya Ya Kwanta Dama Ana Tsaka Da Wasa
A wani labarin na daban, wani ɗan wasan ƙwallon kafa na Najeriya ya kwanta dama bayan ya faɗi ana tsaka da wasa.
Ado Hadi, mai shekara 21, wanda yake bugawa kulob ɗin CD Madridejos a rukunin Terceira na ƙasar Spain, ya faɗi kawai inda yace ga garin ku nan ana tsaka da wasa tsakanin kulob ɗin sa da SP Cabanillas a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairun 2023.