Tsohon kyaftin din Super Eagles, Austin ‘Jay Jay’ Okocha, ya bayyana dalilin da ya sa bai bugawa manyan kungiyoyi Turai wasa ba a lokacin da yake buga wasa,Daily Post ta rawaito.
A cewarsa, manyan kungiyoyin ba su ba shi kwangiloli masu tsoka ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Karshe, Chelsea Ta Nada Sabon Koci
Okocha ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise TV.
Ya kuma yarda cewa zabin kungiyoyi na iya hana shi zama gwarzon dan kwallon kafan Afrika.
Okocha ya taka leda a Frankfurt, Fenerbahce, Paris Saint-Germain Bolton Wanderers, Qatar SC da Hull City kafin ya yi ritaya a shekarar 2008 yana da shekaru 34.
An zabe shi a matsayin gwarzon dan kwallon Afrika a shekarar 1998 kuma ya zo na uku a 2003 da 2004.
“Ba abu ne mai sauki dan wasan Afirka ya buga wa manyan kungiyoyi wasa ba saboda ba sa biyan albashi mai tsoka.
“Lokacin da suka ba ku kwangila, kuɗaɗen kaɗan ne kawai suke baku saboda suna ganin suna yi muku alheri.
“Wannan shine dalilin da ya sa na je kungiyoyin da ke shirye su biya ni mafi girman albashi. Dole na yi watsi da wasu tayi daga manyan kungiyoyi wasanni saboda matsalar albashi.
“Amma yanzu abubuwa sun canza, yayin da ’yan Afirka da ’yan Najeriya ke samun manyan kwangiloli a ketare.”
A wani labarin kuma, Sunayen Yan wasa 5 Da Ka Iya Lashe Kyautar Ballon d’Or
An bayyana sunayen manyan ‘yan wasa biyar da ka iya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana.
Kyautar Ballon d’Or ta kasance kyautar mutum daya da aka fi badawa ga ‘yan wasan kwallon kafa kuma Mujallar labaran Faransa ‘France Football’ ce ke bayar da ita.