Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya bada dalilan da suka sanya har yanzu Najeriya ke yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.
Mustapha yace Najeriya har yanzu bata yi garambawul a ɓangaren Sojojin ta ba.
Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da ya karɓi kwamitin mutum 24 akan bada shawara akan canje-canje a ɓangaren Soji a Abuja.

A cewar sa, yanayin yadda ƙasar take, dole sai an sake canje-canje a ɓangaren tsaro.
Mustapha yace ” garambawul abune dake da wahala a aikata, amma matakan da Ma’aikatar tsaro ta ɗauka abune mai kyau domin magance matsalolin tsaro.
“A shirye nake na bada gudunmawa domin yin garambawul a ɓangaren Soji domin samun cigaba.
Idan dai ba’a manta ba, kwamitin wanda Alwali Kazir ke jagoranta, a watan Satumba Ministan Tsaro Bashir Magashi ya rantsar dasu, domin gano shawarwarin daya kamata abi wajen yiwa sojoji garambawul.