Dalilin da yasa Kwankwaso ke goyon bayan Tinubu ya zaman Shugaban Ƙasa – Deji Adeyanju
Wani dan fafutuka mazaunin Abuja, Deji Adeyanju, ya yi zargin cewa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso na goyon bayan takwaran sa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu.
Adeyanju ya ce Kwankwaso ya yi imanin cewa Tinubu ne zai sa shi ya zama Shugaban Ƙasa idan ya ci zaɓe a 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanatocin APC sun goyi bayan yunƙurin tsige Buhari – Sanata Bulkachuwa
Ya yi nuni da cewa za a ɗauki Ɗan Takarar Shugaban kasa na Kudu da Arewa shekaru 16 kafin ya mulki Najeriya idan Tinubu ya ci zabe a 2023.
A cikin jerin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, Adeyanju: “Idan Tinubu ya zama Shugaban Ƙasa, zai ɗauki wani dan takarar shugaban kasa daga Kudu shekaru 16 ya zama Shugaban Ƙasa kuma daya ga Ɗan Takarar Arewa.
“Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa Kwankwaso ke goyon bayan Tinubu. Yana ganin Asiwaju zai taimaka masa ya samu mulki nan da shekaru 8.
“Muhimmiyar darasi da na koya daga wannan shi ne cewa a rage yanke kauna game da mulki. Wannan shi ne dalilin da ya sa Kwankwaso da Obi ba za su iya aiki tare ba yayin da a bayyane yake mutum daya ne kawai zai iya zama shugaban kasa.