Wani mai fashin baki kuma masanin tattalin arziki Farfesa Ken Ife, ya ce manufar hada-hadar kudi ta babban bankin Kasa CBN ba ta aiki saboda kashi 80 cikin 100 na kudin kasar ba sa yawo.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Ife ya bayyana hakan ne a yayin wani taron lakca karo na 10 na Jami’ar Godfrey Okoye, Enugu, a ranar Juma’a, mai taken “Nigeria: The State of Macro-Economy” wato Kasa Mafi Girman Tattalin Arziki.
A cewarsa, kashi 40 cikin 100 na kudaden kasar ba a banki suke ba yayin da kashi 40 na ‘yan kasar ke fama da talauci.
KARANTA KUMA CBN Ya Bayyana Himmarsa Ta Kare Manyfar Al’ummar karkara
Ya ce wadannan kaso 80 na kudaden da ya kai Naira tiriliyan 2.6 da ya kamata su zo wa bankunan kasuwanci su ba da rance ga kamfanoni masu zaman kansu don samar da ayyukan yi, ba sa zuwar musu, ta haka ne suka durkusar da tattalin arziki.
“Suna hana karfin tattalin arzikin ya samar da ayyukan yi kuma ba mu san nawa ne ke yawo ba kamar yadda fasaha ta kama mu.
“Sake fasalin Naira ya kamata ya zama duk shekara biyar ko wani abu kamar haka, amma shekara 20 ba mu yi ba,” in ji shi.
Ife, wanda shi ne babban mashawarci na hukumar ECOWAS, ya bayyana cewa jabun kudaden da ake yawo da su na iya haura kudaden halak, wanda hakan ya sa CBN ba zai iya sanin nawa ne ke yawo ba.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Masanin tattalin arzikin ya kara da cewa ayyukan masu safarar kudade da manufofin kungiyar ECOWAS su ma sun sanya ana amfani da Naira a wasu kasashe ba tare da sanya ido ba.
A Wani Labarin Kuma Rikicin PDP: Ayu Ba Zai Iya Jagorantar Yakin Neman Zaben Jihar Rivers Ba – Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya dage cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorcha Ayu, ba zai iya jagorantar jihar wajen yakin neman zaben 2023 ba.
Wike ya yi wannan maganar ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na jihar Ribas na 2022 tare da kaddamar da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Sim Fubara, a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, ranar Asabar.