Ministan harkokin lafiya Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu dauke da cutar sarke numfashi basu yarda suna dauke da cutar ba saboda rashin ganin wasu alamu a tattare da su.
Ministan yace “Kaso 80 na masu dauke da cutar COVID19, suna rayuwa ne ba tare da wasu alamu sun nuna sun dauke da kwayar cutar ba”.
Shi yasa yake abu mai wahalar gaske wajen gamsar da su cewa suna dauke da cutar.
Ya kara da cewa “da yawa daga cikinsu basa amincewa a killace su, sun fi so ace sun ji dukkanin wasu alamu dake nuna suna dauke da cutar kafin su aminta a killace a cibiyoyin da aka tanada”.
https://dimokuradiyya.com.ng/labari-cikin-hotuna-yadda-shugaba-buhari-ya-gabatar-da-sallar-jumaa/
“Wasu kuwa duk da sun tabbatar da alamun cutar a tattare da su, basa zuwa yin gwaji face ma killace domin dakile cutar, sai dai su boye gaskiyar al’amarin ta yadda zasu cigaba da rayuwa da ita ba tare da kowa ya sani ba”.
A cewarsa, Ministan ya bayyana cewa wasu da cikin masu jinyar sun tsere daga cibiyoyin da aka killace su ciki kuwa har da jihohin Kano, Legas da kuma Gombe.
Daga bangarensa wani likita mai suna John Oghenehero, ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu dauke da cutar COVID19 na guduwa ne daga cibiyoyin killace mutane saboda gudun tsangwamar da zasu iya fuskata a yayin da suka koma rayuwarsu ta yau kullum.