Gwamnan Jihar Edo Mista Godwin Obaseki ya bayyana dalilin da yasa ya kaiwa Jagoran Jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ziyara.
Hakan ya biyo bayan rade-radin da ake na cewa gwamnan ya mallaki fom din takarar gwamnan jihar a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, sakamakon sabanin da ya samu da tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole.
Sai dai Obaseki ya gargadi shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da kada ya kuskura ya tsoma hannunsa a zaben fidda gwani da Jam’iyyar zata yi a ranar 22 ga watan da muke ciki.
A yayin da yake bayyana dalilin ziyarar tasa yace “na kaiwa Tinubu ziyara domin bana so wani abu ya samu jam’iyyarmu, bana so a samu rarrabuwar kai, saboda ni mutum ne mai son zaman lafiya”.
https://dimokuradiyya.com.ng/kada-ka-kuskura-ka-tsoma-hannunka-a-zaben-fidda-gwani-da-za-a-yi-gwamna-obaseki/
“Dani da abokan takarata ba zamu so mu ga Jam’iyyar da muka gina da rushe ba saboda wani ra’ayi namu na kashin kanmu, shi yasa nake so naga an samu masalaha kuma an yi komai cikin lumana”.
“Wannan shi ne dalilin ziyarar dana kaiwa Tinubu, domin na kara tabbatar masa da cewa muna nan a jam’iyyar APC, kuma shirye muke wajen kawo mata ci gaba, saboda kafin yanzu jam’iyyar na da jihohi 26 amma yanzu mun dawo jihohi 20, dan haka ba zamu bari wani abu ya faru ba face yiwa jam’iyyar nan hidima domin samun ci gaba da kuma hadin kan kasarmu baki daya”.
“Daga karshe ina fatan neman zaman lafiya musamman a jiharmu kuma ina fatan zamu samu wannan zaman lafiyar da fahimtar juna”.