Tsohon dan majalisar dattawa na Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa dalilin da ya sa masu aikata laifuka ke kai hari tare da kona ofisoshi da sauran cibiyoyin hukumar zabe ta kasa (INEC) shi ne yin zagon kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa, ‘Yan bindiga sun yi ta kai hare-hare tare da kona kayayyaki a ofisohin hukumar INEC a fadin kasar nan, musamman a yankin Kudu maso Gabas.
Jaridar Vanguard ta tattaro a jiya cewa wasu ‘yan daba sun kona ofishin INEC da ke karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi ranar Lahadi.
Wasu daga cikin kadarorin da aka lalata sun hada da akwatunan zabe 340, injinan wutar lantarki 14, kayayyakin zabe 130, manyan tankunan ajiya na ruwa, kayan ofis da kuma dimbin katunan zabe.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shehu Sani a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin ya ce maharan makiyan ci gaba ne da ba sa son a gudanar da babban zabe a shekarar 2023.
Ya ce, “Babban makasudin masu kai hari da kona ofisoshin INEC shi ne yin zagon kasa a babban zabe mai zuwa.
“Su makiyan dimokradiyya ne. Hakki ne na kishin kasa mutane su bijire wa tashin hankali kuma su tashi tsaya a kan wadancan ‘yan mulkin kama karya.”
A Wani Labarin Kuma Aisha Buhari: Abin Da ‘Yan Siyasar Arewa Zasu Koya Daga Na Kudu Maso Yamma
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga shugabannin Arewa da su yi koyi daga takwarorinsu na Kudu maso Yamma wajen dora mata a matsayin mataimakan gwamnoni.
Ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan rikicin da ya barke a jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa.