Rundunar Sojin Ƙasa tace dakarunta sun kashe ƴan Ƙungiyar Awaren Inyamurai ta IPOB guda huɗu ɗauke da makamai, wanda suka kaiwa sojoji hari a Jahar Anambra a ranar Juma’a.
Wannan na zuwa ne a yayinda Soji suka ƙalubalanci ƙungiyar da ɗaukar makamai domin haifar da tsoro ga al’umma, gabanin zaɓen Gwamnan Anambra na ranar 6 ga watan Nuwamba a Jahar.
Acewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaru na Soji Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ƴan ƙungiyar IPOB sun kai hari ga dakarun soji dake shatale-talen Ekwulobia na ƙaramar hukumar Aguata ta Jahar Anambra, inda suka kuma ruga bayan sun kai harin.

KARANTA WANNAN LABARIN: Enugu Rangers ta ɗauki Sabbin Ƴan wasa 13 Domin tunkarar Wasannin 2021/2022
Ya ƙara dacewa, dakarun sun bi bayan ƴan ta’addan, inda suka yi musayar wuta, yana mai bayyana rashin jindaɗi na yadda jami’in tsaro guda ɗaya ya rasa ransa.
“Wannan hari ga hukumomin tsaro dake a shatale-talen Ekwulobia na ƙaramar hukumar Aguata ta Jahar Anambara, ya sanya dakarun soji suka yi saurin kai ɗauki a wurin tare da musayar wuta, wanda ya haifar da kisan mutum 4.
Yace dakarun sojin sun kuma samo bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, da wata babbar bindiga da sauran su.