Hukumar lura da aikin ‘yan sanda ta kasar nan ta maye gurbin Hajiya Naja’atu Mohammed, a matsayin ɗaya daga cikin masu sanya idanu na hukumar da za su lura da ayyukan ‘yan sanda a yankin arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an janyo hankalin hukumar ne kan wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja’atu na goyon bayan wata jam’iyya don haka APC take gani ba za ta yi wa jam’iyyar adalci ba. Jaridar Punch ta rahoto.
KU KARANTA: Ganduje Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Kayan Abinci Ga Kanawa
A sanarwar da APC ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar Festus Keyamo ya yi watsi da naɗin Hajiya Naja’atu a matsayin mai lura da ayyukan ‘yan sanda a lokutan zaɓen ƙasar.
Sanarwar da hukumar ‘yan sandan ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton ‘yan sandan ƙasa Bawa Lawan domin lura da ayyukan ‘yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.
Hukumar ta ce a koda yaushe tana taka-tsan-tsan a ayyukanta kuma za ta ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da wanzuwa dimokradiyya a ƙasar.
Haka kuma ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da samun sahihin zaɓe a ƙasa nan.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa hukumar ta sanar da nadin Naja’atu da karin wasu mutane 44, domin sanya ido kan yadda jami’an yan sanda zasu gudanar da ayyukan su a yayin zaben 2023.
A wani labarin kuma: Har Abada Ba Zan Koma Real Madrid Da Yin Kwallo Ba — Raphinha
Dan wasan gaban Kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona Raphael Dias Belloli Raphinha ya bayyana cewa, ba zai ta ba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasa ba, har karshen rayuwarsa. Kamar yadda Fabrizio Romano ya ruwaito.
Mai shekaru 26 Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyi a kafar yada labarai ta Adri Contreras a yau Litinin.