Gwamnatin tarayya a ranar Litinin, ta sanar da dalilinta na kin dakatar da mataimakin Shugaban Yan sanda na Kasa bayan nada shugaban Yan sanda na Kasa baki daya Usman Baba Alkali. Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Sunyi wannan magana ne lokacin da ake karawa kwamishinoni ashirin da hudu girma zuwa mukamin mataimakin Shugaban Yan sanda, a babban Ofishin jami’an Yan sanda ta Kasa.
Muhammad Maigari Dingyadi, yace yanayin rashin tsaro da yayi kamari a kasar ne ya sanya muka bar manyan jami’an Yan sandan.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, babu wani babban Jami’in Dan sanda da yakai mukamin DIGs ko AIGs wanda aka dakatar dashi bayan sanar da zaben shugaban Yan sanda na Kasa IGP, wanda hakan ya sha bambam kan tsarin jami’an Yan sanda.
Muhammad Maigari Dingyadi yace, wannan shine karo na farko da hukumar ta sami wannan cigaban a tarihin kafuwar hukumar.
Yace “gwamnati tayi wannan ne saboda samar da masu hikima da basiran aiki cikin hukumar, yace barin wadannan cikin hukumar zai kawo cigaba sosai wajan kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.”
Ministan yace matakan da ake bi wajan zaben AIG ya hada da gwarzantaka, iya gudanar da aiki, nusar da sabbin AIGs wajan gudanar da aikinsu.
Yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawari albashin ma’aikatan zai fito ta sabon tsarin da aka gabatar.
Kamar yadda yace “Wanda ya bada dayawa, shi zai tsammaci ya samu dayawa, dole jami’ai su kara zage damtse wajan shawo kan matsalar tsaro dake addabar kasar nan, ana tsammanin abubuwa da dama daga gareku wanda zai zama hanya mafi sauki wajan samar da ingantaccen tsaro a gaba daya kasar nan.”
Comments 2