Damfara: Kotu ta ɗaure Hafsan Soji na Boge daya ƙware wajen kwaikwayar sa hannun Buhari, Obasanjo shekara 7
Wata Kotu a Ikeja mai kula da shari’u na musamman a ranar Alhamis ta ɗaure Janar na Soji amma na bogi, Bolarinwa Abiodun, Wanda Sunan sa na gaskiya shine Hassan Ayinde shekaru bakwai, sakamakon laifin sojin gona da kuma Damfarar Miliyan 266.5.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sama da Ƴan Najeriya 3,600 zasu rasa halartar Hajjin Bana
Abiodun ya bayyana kansa a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa domin yin damfarar miliyan 266.5.
Ƙamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya bada rahoton cewa an kama Abiodun dumu-dumu da laifin sa akan wata ƙara daya karbi kuɗi ta hanyar nuna kansa alhali na karya ne, bayan Hukumar Hana Zagon Ƙasa EFCC ta kama shi a ranar Alhamis.
Da yake ƙaddamar da hukuncin, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo ya yanke hukuncin gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara biyo bayan kama shi da laifi.
Ya ce “wanda ake zargin yana bayyana kansa a matsayin Janar na Soji, wanda yake kwaikwayon Sa hannun tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, da kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wajen damfarar mutane.
Ya ƙware wajen damfarar mutane saboda ilmin sa, wanda wani zaiyi mamaki idan aka ƙyale shi. Abun baƙin ciki ne mutane irin wannan suna bata suna kasar nan.
“A dalilin haka, na zartar maka da hukunci kai Bolarinwa Abiodun hukuncin Shekaru 7 ba tare da zaɓin biyan tara ba.