Kotu a Ƙasar Amurka a ranar 14 ga watan Fabrairu ake sa ran Kotu zata tura Fitaccen Ɗan Social media Ramon Abbas Olorunwa da aka fi sani da Hushpuppi sakamakon badaƙalar Dala Miliyan $24 da ake zargin sa.
Wasu hujjoji sun nuna cewa Hushpuppi zai fuskanci shekaru 20 a gidan yari, kuma zai fuskanci hukunci akan haka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rahoton TI Ya Nuna Jam’iyyar APC Mafaka Ce Ta Cin Hanci Da Rashawa- Shugaban Marasa Rinjaye
A cewar wata kafa ta zamani, Hushpuppi zai san makomar sa a ranar Masoya, bayan an tsare shi na tsawon shekaru biyu a Dubai, Daular Larabawa da Los Angeles na Ƙasar Amurka.
An dai tabbatar da laifin sa a ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 2021, kuma sashen Shari’a na Amurka ya tabbatar da ranar a Email ranar Talata 25 ga watan Janairun shekarar 2022.
Hushpuppi yayi ƙaurin suna wajen tura hotunan shi na daular dayake ciki, inda yake da mabiya har miliyan 2.5.
Hujjoji dake gaban Kotu a California sun tabbatar da cewa ta’addancin Hushpuppi yakai na almundahanar kusan Dala Miliyan $24.
Comments 1