Hukumar yaki da rashawa ta Nijeriya wato EFCC ta shawarci matasan Nijeriya musamman dalibai da su nisanta kawukansu da ayyukan da ka iya kawo musu tarnaki a rayuwarsu ta gaba.
Isyaku Sharu, shugaban ofishin EFCC din a Ilorin, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a yayin da yake gabatar da jawabi ga daliban Jami’ar Ilorin.
Sharu ya ce wannan kiran ya zama wajibi ne musamman idan aka yi duba da yadda ayyukan damfara a shafukan Intanet da aka fi sani da “Yahoo-Yahoo”, ke yawaita a kowacce rana, kuma ya ce hakan na faruwa ne a tsakanin matasa.
Ya ci gaba da cewa mafi yawan wadanda hukumar ke zargi kuma take gudanar da bincike akan su dangane da ayyukan damfarar dalibai ne da suka fito daga makarantun gaba da Sakandare a fadin Nijeriya.
Sharu ya ce hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doron dokokin Nijeriya wajen ganin ta dakile ayyukan bata gari a kasar musamman abin da ya shafi ta’ammuli da kudade a kasar. Ya ce ya damu kwarai da gaske yadda ya ga adadin daliban da suka fada irin wannan harkar wajen damafar wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Sharu ya nemi daliban da su mayar da hankali wajen karatunsu, sannan ka da su zama sun sanya a ransu cewa su suna son yin kudi nan da nan ne, wanda ya ce; wannann tunanin ne ke sanya da yawan matasa fadawa harkar damfara da sauran mugayen ayyuka. Ya ce wadanda suka riki gaskiya tare da jajircewa; “tabbas za su ga nasara a rayuwarsu.” Ya tabbatar.
A karshe ya nemi da su zama masu da’a tare da bin doka da oda a kasa. Inda ya ce hukumar ba ruwanta da shekarun wanda ake zargi da aikata laifi. Ya karkare batunsa da tabbatar da cewa hukumar EFCC din za ta ci gaba da yaki da rashawa da cin hanci a Nijeriya har sai sun cimma manufa.