Babban Bankin Nijeriya, CBN ya sha alwashin tallafa wa manoma domin tabbatar da ganin an samu amfani mai yawa a noman bana. CBN za ta agazawa manoman dake tsarin shirin gwamnati na ‘Anchor Borrowers Programme (ABP)’ akalla su miliyan daya da dubu dari shida.
Jami’in CBN Yila Yusuf ne ya sanar da hakan a ranar Talata a taron raba wa manoman auduga a garin Kwali a Abuja. “Gwamnati za ta tallafawa manoman auduga 256,000 ta tsarin shirin ta na ABP domin karfafa guiwowin manoman auduga a kasar nan.” inji shi.
Manoman dake karkashin shirin ABP na samun tallafin kayan aikin noma a matsayin bashi wanda za su biya da zarar sun yi girbi.
A farkon shirin ABP gwamnati ta raba wa kananan manoman da suka yi rijista da shirin Naira biliyan 220 a kasar nan.
Da yawa daga cikin wadanda suka karbi bashin kudin ba su iya biyan wannan basussuka da suka karba ba da hakan yasa a bana a ka rage ribar.