Daga cikin Kwamishinoni 23 da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya rantsar a shekaranjiya Litinin, harda dan agajin Izala daga bangaren Jos.
Jaridar Dimokuradiyya ta tabbatar da cewa; Gwamnan Lalong ya nada tare da rantsar da Alhaji Muhammad Muhammad Abubakar, a matsayin Kwamishinan sufuri wato ‘Transport’a turance.
Shi dai Alhaji Muhammad ya kasance Dan Izalan ne bangaren Shaikh Sani Yahaya Jingiri, inda wadansu rahotanni ke rade-radin cewa; Shehin Malamin ne ma ya ba da sunansa domin ganin an nada shi a matsayin Kwamishina.