Akalla mutane 20 aka tabbatar da mutuwarsu bayan harin dan bindigan da ya bude wuta kan masu siyayya a wani shagon zamani da ke yankin El Paso na jihar Texas a Amurka. Harin wanda ya faru a ranar Asabar tuni aka fara alakanta shi da na nuna kyama. Tuni dai Jami’an ‘yan sanda suka kame mutumin da ya kaddamar da harin yayin da suka ce za a fara yi masa tuhuma. Harin wanda shi ne na baya-bayan nan da aka kaddamar a kasar ta Amurka mai fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga wanda ke da nasaba da nuna wariya ko kuma kyama ya kuma jikkata mutane 26. Tuni dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump da gwamnan jihar ta Texas suka yi tir da harin yayin da jami’an tsaro suka ce suna ci gaba da gudanar da bincike bayan kame maharin. Harin dai shi ne irinsa na biyu cikin mako guda a irin shagunan zamanin, haka zalika ya zo ne bai wuce kwanaki 7 dafaruwar makamancinsa a jihar California ba.