Alkali Mojisola Dada na kotun musamman dake Ikeja a jihar Legas a ranar Alhamis ya nemi wanda aka yankewa hukunci kan zarginsa da damfarar kudi ta Intanet da ya maidawa gwamnatin tarayyar Nijeriya naira miliyan 29.2 da aka kama shi da su a yayin binciken EFCC.
An kama shi ne da naira miliyan 29.2 a yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa na EFCC suke bincike.
An zarge shi da aikata laifuka biyu wanda ya hada da kulla makirci da kuma satar kayan da ba na shi ba.
Mai shari’a Mojisola Dada na kotun har wala yau ya aika da Chibundu Anuebunwa gidan yari na shekara daya bisa samunsa da laifin.
Sai dai mai Shari’a Dada ya nemi da kuma ya biya tarar naira miliyan 1.5 bisa aikata laifin.
“Wanda ake zargi bai batawa kotu lokacinta ba wajen amsa laifinsa, kuma wannan shi ne laifinsa na farko. A don haka na yanke masa hukuncin gidan yari na shekara daya da kuma biyan tarar naira miliyan 1.5.” in ji Alkalin.