Wani Dan aware a Jam’iyar APC Mai Mulki ya bukaci Babban Kotun kasa, dake Babban birnin tarayya Abuja, da ta rushe Kwamitin ruko na jam’iyar, da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ke jagoranta.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata Kara da Okosisi Emeka Ngwu ya shigar a gaban Kotun, Mai dauke da Lamba: FCT/HC/CV/1824/2021, Kuma dauke da ranar 2 gawatan Ogustan shekarar 2021. Inda takaddar karar, ke dauke da sunayen jagororin Kwamitin a matsayin wadanda ake kara.
Sunayen su ne: Mai Mala Buni, Isiaka Oyebola, Ken Nnamani, Stella Okorete, Governor Sani Bello, Dr James Lalu, Senator Abubakar Yusuf, Hon. Akenyemi Olaide, David Leon, Abba Ali, Prof. Tahir Mamman, Ismail Ahmed da kuma Sanata Akpan Udoedehe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutum 8 a Niger
Lauyan Mai shigar da kara Chief Oba Maduabuchi SAN, ya kuma bukaci Kotun da ta rushe Kwamitin rukon kwaryan jagorancin jam’iyar APC, domin kuwa, babu wani sashi na dokar jam’iyar da ya sahale wa Kwamitin.
Kazalika ya Kuma bayyana cewa sashi na 87 (4) (B)(1), na tsarin kwamitin gudanar wa na Kasa wato NEC, ya bai wa jam’iyar siyasa damar nada Gwamna, ko wani Dan’takara, jagorancin jam’iya, domin sanya ranar zaben fidda gwani a Jam’iyar.
Sai dai har izuwa hada wannan rahoton, ba’a sanya ranar da Babban Kotun za ta fara sauraran karar ba.
Comments 1