Mazauna karamar hukumar Geidam a jihar Yobe sun yi alhinin rasuwar Hakimin Laruski Ibrahim Tijjani Saleh kuma dan Sarkin Gazargamu, Alhaji Tijjani Saleh Geidam.
Sarkin ne ya tabbatar da rasuwar dansa ta hanyar sakon da ya aike wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya.
Wata majiya ta iyalin marigayin ta ce yariman ya rasu ne sakamakon hatsarin babur mai kafa uku (Keke Napep) a ranar Lahadi a garin Maiduguri Babban Birnin jihar Borno.
Ya ce, “An garzaya da hakimin asibitin koyarwa na Maiduguri da gaggawa bayan faruwar lamarin, amma abin takaici mun rasa shi.”
“Ya rasu Yana da shekaru 30, kuma ya bar mata daya da ‘ya’ya biyu”.
Abokansa sun bayyana rasuwar hakimin a matsayin babban rashi ga al’ummar gundumar Laruski da masarautar Gazargamu da jihar Yobe da ma kasa baki daya.
Mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Suleiman, ya jajantawa al’ummar Masarautar Gazargamu, inda ya ce za a rika tunawa da marigayin Kuma Hakimin, bisa martabarsa da mutuncinsa da kuma kaunarsa marar iyaka ga al’ummarsa da jajircewa wajen kyautata rayuwarsu da ci gabansu.