Dan majalisarr tarayya, Alhaji Kabiru Maipalace, mai wakilar Gusau/Tsafe a jihar Zamfara yana daukar nauyin horas da mata 100 daga yankin da yake wakilta domin horas da su yadda ake kiwon kaji.
Alhaji Kabiru ya bayyana hakan ne a Gusau a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Litinin. Dan majalisar ya ce; wadanda suka amfana da wannan horaswar, suna ci gaba da karbar horo a wani shirinsa na samar wa da mata ayyukan yi. A cewarsa, bayan an kammala horas da su, za a bai wa wadanda suka amfana da shirin kudade da kuma kaji 100 ga kowannensu domin ganin an tallafa musu wajen yin kiwon kajin.
Ya tabbatar da cewa; yana kuma shirye-shiryen ganin ya fadada shirin a nan gaba domin akalla a horas da mata 500 a bangarori samar da ayyukan yi daban-daban.
Ya kara da cewa; wata uku da ya wuce, an horas da mata 120 a karamar hukumar Tsafe. Ya ce bayan koyawa al’umma ayyukan yi, bangaren ilimi ma zai ba shi muhimmanci. Ya ce; a karkashin shirin ilimi, ya dauki nauyin dalibai 1000 a matakin Sakandare wanda ya hada maza da mata musamman wadanda suka fadi jarabawar kammala Sakandare, wato SSCE inda za su sake rubuta jarabawar.