- Francis Ottah yace zai gabatar da wani kudiri dazai bada damar yin gwajin kwaya ga yan siyasa a Najeriya
- Wannan kudirin dai zai bada damar gudanar da gwajin kwaya ga jami’an tsaro da matasa masu neman guraben karatu a Najeriya
- Ya alakanta yadda kwaya ke taimakawa wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a kasar
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki ta Kasa akan hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Francis Ottah yace zai gabatar da wani kudiri dazai sanya Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta rika yin gwajin Kwaya lokaci zuwa lokaci, ga duk Wanda ke neman kujerar siyasa a Najeriya.
A cewar sa kudirin zai Kuma baiwa Hukumar damar gudanar da gwajin kwaya ga Jami’an tsaro, gami da Daliban dake neman guraben karatu a Manyan Makarantun Najeriya ya zama dole sai anyi masu gwajin Kwaya.
Dan Majalisar a jawabin daya fitar a ranar Litinin a tabakin mai taimaka masa akan Kafafen Yada Labaru Andrew Agbese, yace illolin kamuwa da cutar Shan miyagun kwayoyi ya fantsama a dukkanin bangarori na Al’umma, kuma gwajin Kwaya ne kadai zai iya wayarwa mutane Kai akan matsalar dake tattare da shan miyagun kwayoyin, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: An Dakatar Da Shugaban Marasa Rinjaye Na Jihar Nasarawa
Ya bayyana cewa, yadda wasu Yan siyasa ke canja halayyar su gami da yawaitar ayyukan ta’addanci da ake yi a cikin Al’umma dukkanin su kwaya ce ta haifar su.
Ya jaddada cewa, za’a iya magance hakan idan ya zaman to wadanda suke fama da matsalar basa cikin masu Shan miyagun kwayoyi.
“Ina gabatar da kudiri dazai baiwa Hukumar Hana Shan miyagun kwayoyi ta Kasa, damar gudanar da gwaji ga dukkanin yan siyasa, da manyan ma’aikatan gwamnati, da Sojoji da sauran Hukumomin tsaro, gami da Matasa masu neman guraben karatu a Manyan Makarantun Kasa. Wannan zai kawo karshen hauka da ake yi a bangarorin gami da wayar wa Al’umma kai.
“Shan miyagun kwayoyi abune wanda ya mamaye ko’ina a cikin Al’umma, daga Makarantun Sakandire zuwa Jami’o’i, daga Arewa zuwa kudu, daga Yan siyasa zuwa Ma’aikatan Gwamnati. A takaice Najeriya itace kasa data fi kowace yawan masu Shan miyagun kwayoyi, kuma Tabar wiwi ita tafi yawaita a Kasar,”inji shi.