Dan majalisar tarayya na jam’iyyar APC mai wakiltar Chibok, Damboa da Gwoza dake jihar Borno, ya nemi gafarar zancensa da yake cewa rashin yin kyakkyawan shiga ne ke janyo fyade.
Jaha wanda ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da ‘yan jarida a ranar Asabar a Abuja, ya ce maganar nasa da ya yi a yayin muhawara a majalisar na cewa rashin sanya tufafin mutunci ke janyo maza masu fyade na yiwa mata fyaden, ya gano ya yi kuskure, kuskuren da ya batawa ‘yan Nijeriya rai, da kuma sauran al’umma, musamman mata wadanda suke Iyaye ne, mata ne, ‘yan’uwa ne kuma ‘ya’ya ne.
Sai dai ya ce har yanzu yana kan ra’ayin tabbatar da ganin cewa ana yankewa masu fyade hukuncin kisa.
Amma ya ce yana mai bada hakurin cewa rashin shigar mutunci ne ke jawo fyade, inda ya ce bai kamata ya yi zancen ba saboda a karshe dai mata ake cutarwa, kuma a lokaci guda su ake zargi, wanda ya ce sam hakan bai dace ba.