By Abbas Yakubu Yaura
Sanata Binos Yaroe, dan jam’iyyar PDP mai wakiltar Adamawa ta Kudu, ya baiwa ‘yan mazabar sa akalla 634 babura, da keken dinki da dai sauransu.
Da yake jawabi yayin kaddamar da bikin a ranar Laraba a Mayo-Belwa, Yaroe ya ce an shirya kayayyakin ne domin tallafawa wadanda suka ci gajiyar tallafin don taimakawa kansu, iyalai da sauran jama’ar da ke kewaye da su.
“A cikin shirin bada tallafin a yau, muna raba babura sama da 100, keken dinki 178, injin nika 48, na’urar firji 39, famfunan ruwa 250 da injinan tayal 9 ga manoma,” inji shi.
Dan majalisar ya ce sauran kayayyakin sun hada da Injin feshin 400 da buhunan taki 186.
Sannan ya ce kowane bangare na mutanen da suka fito daga kananan hukumomi tara na mazabar za su ci gajiyar shirin bada tallafin, musamman jami’an jam’iyyar.
“Saboda wadannan mutanen ne da muka yi aiki da su kuma sun taimaka mana, mun zo nan don gane su.
“A baya, mun yi aikin karfafawa gwiwwa, shirye-shiryen horarwa da kuma wayar da kan jama’a wadanda ba su shafi siyasar jam’iyya ba, amma a wannan karon, zai yi kyau mu gane mutanen da suka yi wa jam’iyyar aiki,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da kayan da aka ba su yadda ya kamata.
A nasa jawabin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Alhaji Abubakar Shehu ya yabawa dan majalisar bisa wannan karimcin.
Sannan ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su samu katin zabe na dindindin (PVCs) domin su samu damar kada kuri’a a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Mista Ismail Hamman, wanda ya ci gajiyar tallafin daga karamar hukumar Ganye, wanda ya samu babur, ya gode wa dan majalisar, inda ya ba shi tabbacin cewa zai yi amfani da kayan aikin yadda ya kamata.