By Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar dokokin jihar Anambra, Onyebuchi Offor, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC yunkurin da ake na tunkarar zaben gwamna da akayi a ranar 6 ga watan Nuwamba, ya koma jam’iyyarsa ta PDP.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Offor, wanda shi ne mamba mai wakiltar mazabar Ekwusigo kuma mai rike da mukamin shugaban marasa rinjaye, ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.
A lokacin da yake sanar da dawowar sa yace, “Wata biyu da suka wuce, na sanar da sauya sheka na daga PDP zuwa APC a zauren majalisar. Na gwada ruwa na gane cewa tsohuwar jam’iyya ta PDP ta fi.Don haka ina son in sanar da wannan majalisa cikin kaskanci cewa zan koma jam’iyyata ta PDP.”
Da yake mayar da martani kan lamarin, dan majalisar mai wakiltar mazabar Ogbaru na jihar Ogbaru, yace “Shigowar ku zuwa APC babbar illa ce ga jam’iyyar PDP a Anambra. Idan da baka sauya sheka ba, da watakila PDP ta yi kyau a zaben gwamna, amma muna yi maka maraba da komawa PDP inda ka ke da gaskiya.”
Mamba mai wakiltar mazabar Idemili-South, Chuka Ezewunne, ya bayyana ficewar Offor a lokacin zaben a matsayin babban jarabawa.Ezenwune ya ce, “A matsayina na wanda ya kafa jam’iyyar PDP, na san Offor da kyau kuma abokin kirki ne, duk da cewa jaraba ce ta jawo shi zuwa APC. Mun yi farin cikin dawowar sa PDP kuma muna kira ga sauran mambobin dasu dawo gida.”
Da yake jawabi, Emeka Aforka, mai wakiltar mazabar Orumba ta Arewa, ya bukaci ‘yan majalisar da suka sauya sheka daga jam’iyyar APGA zuwa APC a lokacin zaben dasu dawo.
Sannan yace, “APGA ce jam’iyyar data yi nasara a Anambra kuma gida ce ga kowa da kowa. Ina kira ga mambobin da suka bar APGA dasu yi koyi da Offor su dawo gida.