Dan majalisar dokokin jihar Adamawa, Shuaibu Babas, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
Shuaibu Babas mai wakiltar mazabar Fufore/Gurin a majalisar ya fice daga babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar yana zargin an tafka kura-kurai a zaben fidda gwani na majalisar dokokin da ya gabata a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.
Dan majalisar a cikin wata wasika da ya aikewa majalisar wanda kakakin majalisar Aminu Iya Abbas ya karanto a zaman da aka dawo ranar Litinin, ya ce rashin adalcin da aka yi masa a zaben fidda gwani na jam’iyyar ya sa ya fice daga APC.
Babas ya ce jam’iyyar APC ta kasa gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya a mazabar sa, kuma ba shi da wani zabi illa ficewa daga jam’iyyar.
Chadi ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye
Shugaban majalisar ya taya shi murnar shiga jam’iyya mai mulki tare da bukatar shi da ya ji cewa tamkar yana gida ne.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, bayan sauya shekar Shuaibu Babas, dan majalisar dokokin Adamawa mai wakilai 25, Jam’iyar PDP ta samu rinjayea a majalissar da mambobi 14 , yayin da APC ke da 10, ita kuma New Nigeria Peoples Party (NNPP) tana da guda daya.
Jam’iyyar NNPP tana da mamba daya a watan da ya gabata lokacin da tsohon shugaban masu rinjaye, Hammantukur Yattusuri ya fice daga PDP zuwa NNPP bayan da ya kasa samun tikitin takarar kujerar majalisar wakilai ta PDP da ya ke nema.