Daga Muhammad Farouk
Dan majalisar tarayya, Tijjani Jobe ya caccaki gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa yunkurin da gwamnan ke yi wajen sauya dan majalisar da dan gwamnan.
Dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa duk a jihar Kano din, ya fara samun matsala da gwamnan da wadansu jigo a jam’iyyar ta APC.
A wani bidiyo na kusan minti goma, Jobe ya bayyana cewa akwai wani mutum barawo da yake son danne masa hakki, inda ya jaddada cewa shi zababben dan majalisar al’umma ne har sau uku. Inda ya ce kuma shi har yanzu dan jam’iyyar APC ne, kuma ya ce idan ya ga damar tsayawa takara a wata jam’iyyar kamar APGA, tabbas shi zai lashe zabe.
“kujerar ba ta gado ba ce, kuma ina da ‘yancin tsayawa takara”. Ya jaddada.