By Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ikwo/Ezza ta kudu a majalisar wakilai ta kasa Hon.Kwamared Chinedu Ogah, a ranar Lahadin da ta gabata, ya raba magunguna da kayan aiki na sama da Naira miliyan 200 kyauta ga mazauna karkara da asibitocin mazabarsa.
A cewarsa, manufar wannan atisayen shine don tabbatar da cewa al’ummar mazabar sa sun samu kulawar jinya da magani kyauta a jihar.
Da yake karin haske ga manema labarai a Abakaliki, Ogah, wanda ya bayyana cewa, kayayyakin kiwon lafiya na hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta kasa ne suka jawo hankalinsu, ya kara da cewa an ware cibiyoyin kiwon lafiya kimanin 20 a mazabarsa domin karbar kayayyakin da kuma tabbatar da mazauna karkara sun samu ba tare da wata tangarda ba.
A cewar sa, “Muna raba kayan aikin asibiti da magunguna ga cibiyoyin lafiya daban-daban a mazabar tarayya ta Ikwo/Ezza ta kudu ta jihar Ebonyi.
“Wadannan magunguna da kayan aikin an jawo su ne ta hanyar Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa da ci gaba, sannan yace wannan wani bangare ne na alkawarin da muka yi wa jama’armu na cewa za mu kula da harkokin kiwon lafiyarsu.yace ana raba wadannan magunguna da kayan aiki ga cibiyoyin lafiya kyauta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Cibiyoyin lafiya da zasu karbi wadannan kayayyakin jinya suna zaune ne a mazabar tarayya ta Ikwo/Ezza ta Kudu, wanda adadin su ya kai kusan 20,sannam adadin magungunan da kayan aikin ya kai kimanin na naira miliyan 200m, Kuna iya gani da kankuma.
Kazalika yace “Sayar da kayan ba zai yiwu ba saboda muna da masu dubawa, Muna da mutanen dake kallon motsa jiki.sannan mata da matasa suna nan a wurin Dattawa suna nan don haka babu yadda za a yi irin wannan abu ya faru a can. Yayin da kasafin kudin shekarr 2022 ke gudana, yawancin abubuwan da muka jawo suma za su bi su.”