Honarabul Jacob Orban mai wakiltar mazabar Katsina-Ala ta yamma a majalisar dokokin jihar Benue ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Sanarwar Ficewar Orban na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Titus Uba kuma mataimakin kakakin majalisar, Rt Hon Christopher Adaji wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Talata, 26 ga watan Yulin shekarar 2022 ya karanta.
Ya bayyana rashin tsarin tafiyar da dimokuradiyyar a cikin gida a jam’iyyar APC a matsayin babban abin da ya sanar da sauya shekarsa, inda ya ce sabanin da aka samu ya haifar da samuwar bangarori da kungiyoyi da dama a cikin jam’iyyar.
Dan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin riko na majalisar dokokin jihar Benue mai kula da al’adu da yawon bude ido, ya bayyana jin dadinsa ga shugabanni da mambobin jam’iyyar APC bisa ba shi damar tsayawa takara a karkashin inuwarta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Sojojin Najeriya Ta Sake Ceto Wasu ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2
Da yake mayar da martani, mataimakin kakakin majalisar, Rt Hon Christopher Adaji, a madadin ‘yan majalissar ya taya wakilin Katsina Ala Ta Yamma murnar ficewa daga jam’iyyar tsintsiya zuwa jam’iyyar PDP tare da ba shi tabbacin samun dama a sabuwar Jam’iyar.
Ficewar Hon Orban zuwa PDP ya kawo adadin ‘ya’yan PDP a Majalisar Jiha zuwa ashirin da shida a halin yanzu.
A wani labari kuma na daban.
Babban Da Ya Kashe Mahaifinsa Kan Filin Gado
A ranar Litinin din da ta gabata ne mazauna garin Masaka da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa suka shiga cikin firgici bayan da dan wani mutum na farko mai suna Tunde Badejo ya daba wa mahaifinsa Badejo Idowu wuka da tayi sanadiyar mutuwar sa har lahira, bisa zargin mallakar wani filin gado.
Jaridar City & Crime ta samu labarin cewa Tunde ya shafe sama da shekara guda yana cin zarafin mahaifinsa.
A lokacin da wakilin Jaridar Daiky Trust ya ziyarci wurin, matar marigayin Madam Tolani Badejo, ta ce mijinta ya nemi Tunde da ya ba shi lokaci domin ya raba fili cikin adalci tsakanin shi da sauran ‘yan uwasa.
Ta bayyana cewa, “Ya kasance a wuyan mijina don filin tun bara. Don haka a gardamarsu ta karshe a ranar Litinin, ya zaro wuka ya daba wa mahaifinsa sau da yawa a kai, wuya, kirji, hannaye da kafafuwansa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Inda na daga murya sai ya gudu.”
Dan marigayin na biyu, Ayomide Badejo, ya ce an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda yayin da aka ajiye gawar mahaifinsa a dakin ajiyar gawa.