Tsohon dan Sandar Minneapolis da aka samu da Laifin kisar bakar fatar nan George Floyd ya bukaci da a sake wata sabuwar shari’a fill a ledar ta.
Lauyoyin Derek Chauvin sun mika sabon kundin bayanai gaban kotu kan cewa an aikata ba daidai ba yayin shari’ar da aka yi mishi wanda ta kai ga an daure shi.
An samu Mista Chauvin ne da laifin kisar kai da kuma yaka mutum bayan da aka hasko shi a wani faifan bidiyo mai mintuna tara danne da wuyar Mista Floyd.
Lauyoyin sa sun ce wanda suke karewar yana da yancin a yi mishi adalci yayin shari’ar.
Wannan al’amari na Mista Chauvin ya kasance abin kunya ga Amurkawa, to sai da sun jinina qa kokarin gwamnati bisa tsayuwar daka wajen ganin an yi adalci wa wanda aka hallaka.
Mista Chauvin wanda aka yanke mishi hukunci daurin shekaru arba’in a gidan yari za a garkame shi ne a watan gobe.