Dan Sarkin Kano Aminu Bayero ya nemi auren diyar shahararren dan siyasa kuma dan kasuwa a jihar Sakkwato, mai suna Ummarun Kwabo.
Kabiru Bayero, wanda ya kammala karatun harkokin kasuwanci, kuma shi ne babban dan sarkin. Kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito, cewa wata babbar tawaga daga Masarautar Kano da Bichi ta isa Sokoto a ranar Asabar din da ta gabata domin neman auren Aisha Ummarun Kwabo da Kabiru Aminu Bayero.
Tawagar Kano karkashin jagorancin Wazirin Kano Sa’ad Gidado, sun hada da Sarkin Dawaki Maituta na Kano, da Abubakar Bello Tuta; Dan Isan Kano, sai Kabiru Tijjani Hashim; Dandarman Kano, da kuma Bello Bayero, Kachallan Kano, Magajin Galadima.
Jaridar Dimukuradiyya ta ruwaito cewa an gudanar da taron ne a gidan gwamnatin Sokoto, inda wani tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya bayar da amincewar auren (baiko) a madadin iyayen amaryar.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya samu wakilcin Wazirin Sakoto, Sambo Junaidu.
Sannan an biya kudin sadaki Naira 250,000 a gaban shedu.