A jiya ne wata kotu da ke zama a yankin Ebute na Jihar Legas ta tsare wani dan shekara 16 bisa zargin laifin kashe wani yaro.
Shi dai wannan wanda ake zargi an kawo shi kotun ne bisa zargin kisan kai da ya aikata.
Alkaliyar Karamar Kotun, Misis Komolafe A.O ta ce a tsare yaron a gidan gyaran hali na maza dake Oregun na Jihar Legas. inda za a dawo ranar 20 ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraron shari’a.
Dan sanda mai shigar da kara ya ce, wanda a ke zargi da aikata laifin ya yi wannan kisa ne ranar 18 ga watan Oktoba da misalin karfe 2:00 na yamma a madakatar Vespa da ke Ijanikin.
Dan sanda mai kara ya ce, wanda a ke zargin ya bar makarantarsu ne ya tafi makarantar su marigayin, inda suka fara fada, a karshe ya zaro wukar dakin madafar abinci ya soka masa a wuya. wanda hakan ya zama sanadiyyar mutuwarsa.