Daya daga cikin masu neman kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC Mai Mulkk a jihar Yobe, Dr Aji Kolomi, ya yi murabus daga zama mamba a jam’iyyar.
Kolomi, wanda ya tabbatar da murabus dinsa ga wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya a jiya Talata ya ce, yayi hakan ne don mashin kansa.
A cikin wasikar da ya aike wa shugaban mazabarsa, Kolomi ya ce, Murabus din nasa zai fara aiki ne daga ranar Litinin.
“Ina so in mika godiya ta a gare ku, da dukkan majalissa zartarwa na jam’iyyar, saboda iri goyon bayan da kuka bani yayin da na fito zaben fidda gwani na takarar gwamna a shekarar 2019, a don haka nake ci gaba da godiya,” in ji shi a cikin wasikar.
KARANTA WANNAN LABARIN: jihar Yobe ta Amince da Shekaru 65 na yin Ritayan Malaman Makaranta
Ajiko, wanda ya fito daga Gujba karamar hukuma daya da Gwamna Mai Mala Buni, ya ce, nan ba da jimawa ba, zai sanar da matakinsa na gaba game da jam’iyyar da zai koma.
A wani labarin Kuma makamancin wannan.
Wasu daga cikin jami’an jihar da mambobin jam’iyyar PDP a Yobe sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inji rahoton kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN.
Wadanda suka koma APC sun hada da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na jiha, Alhaji Usman Amale, da Mataimakin Sakataren jam’iyar, Malam Ahmadu Biriri.
Gwamna Mai Mala Buni, wanda kuma shine Shugaban riko na Jam’iyar APC, ya gode musu saboda kasancewa cikin masu yunkurin “ceto Nigeria”.
“A yanzu jam’iyyar APC wani yunkuri ne da ke taimakawa kan hadin kai, ci gaban Al’uma da ci gaban Nigeria.
“Muna maraba da manyan ‘yan Nigeria daga kowane fanni na rayuwa, daga fannoni daban-daban, al’adu, addinai da yanayin siyasa.” Inji shi.
“Maganin matsalolin da Nigeria ke fuskanta ya ta’allaka ne da kwanciyar hankalin siyasar kasar; ya kamata dukkanmu mu taru don inganta hadin kanmu don ci gaban kasar ”in ji Mala Buni.
Kazalika ya tabbatar wa masu sauya shekar samun hakkokin su, kamar kowane memba don ba da gudummawa wajan a ci gaban Nigeria.
Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, tsohon mataimakin shugaban PDP, ya ce ba su da wani dalili da ya rage mu na zama a jam’iyar PDP, kuma ya nemi afuwar jinkirin da sukayi na rashin komawa APC akan lokaci.