Wani tsohon dan majalisa a jihar Ekiti kuma mai biyayya ga tsohon gwamna Ayo Fayose, Bisi Kolawole, ya zama dan takarar jam’iyyar PDP na jihar Ekiti a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 18 ga watan Yuni.
Kolawole ya samu kuri’u 671 inda ya doke sauran ‘yan takarar da suka fafata a zaben da suka hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti Cif Segun Oni wanda ya zo na biyu da kuri’u 330 yayin da Farfesa Kolapo Olusola-Eleka tsohon mataimakin gwamna kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna na shekarar 2018 a jihar, ya zo na uku da kuri’u 93.
Sauran sun hada da Adewale Aribisala -56, Deji Ogunsakin -6, Kemi Adewumi -1, yayin da Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi, wanda a baya ya janye daga takarar ya samu kuri’u 2.
Daga cikin wakilai 1,208 da aka amince da su, jimillar kuri’u 1,185 ne aka kada yayin da kuri’u 13 suka tashi.
A jawabinsa na nasararsa, Kolawole ya yabawa duk wadanda suka gudanar da aikin cikin “yanci da kuma adalci.”