By Abbas Yakubu Yaura
Babban Lauyan Najeriya (SAN) kuma mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar APC, Cif Garba Pwul, ya yi gargadi kan kada kuri’a ga manyan masu neman mukamai a lokacin zaben fidda gwani da zabukan da za a yi dake tafe.
Cif Pwul ya ce idan har mutane suna son a daidaita su, to babu shakka su guji siyasar kudi yayin da yake mayar da martani ga manema labarai a birnin Jos.
Barau Ya Fasa Neman Takarar Gwamna, Zai Fafata Da Ganduje A Kujerar Sanata
Ya ci gaba da cewa, “ Idan za ku lura da cewa al’umma a kullum a lokaci irin wannan suna nadamar zaben buhunan kudin da ake zargin wasu ‘yan siyasa nayi a mukaman shugabanci daban daban.
Ya kara da cewa “amma sai ka ga masu kada kuri’a sun sake yin irin wannan kuskuren a zabuka masu zuwa, kuma tun shekarar 1999 aka fara yin hakan”.
“Batun da na ke yi shi ne, zaben wanda ya fi kowa takara a matsayin shugaban kasa kamar shan guba ne wanda a karshe zai kashe ka idan bakuyi hankali ba”.
A cewar sa “A wannan yanayin idan kuka kuskura kuka sake zabar wanda ya baku kudi, zai kashe tattalin arzikin ku, ya kashe al’ummarku da kashe makomarku da makomar ‘ya’yanku.”
Comments 1